Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

‘Yan bindiga sun hallaka mutane 12 a Afrika ta Tsakiya

Wasu ‘Yan bindiga da ba’a san ko su waye ba sun hallaka mutane 12 a wasu kauyuka da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai fama da tashin hankali, wanda shine irin sa na farko tun bayan zaben Faustin-Archange Touadera a matsayin shugaban kasa.

Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra
Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra REUTERS/Siegfried Modola/Files
Talla

Rahotanni sun ce an kai harin ne a kusa da birnin Bambari, kuma ana danganta shi da masu satar shanu ne amma ba harkokin siyasa ba.

Hukumomin kasar sun ce an kashe mutane 6 a kauyuka 3, cikin su harda mata 3 'yan gida daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.