Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

Ana fama da yunwa a Afrika ta tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya tace ana fama da matsalar karancin abinci a Afrika ta tsakiya inda kusan rabin al’ummar kasar ke fama da yunwa sakamakon rikicin kasar na tsawon shekaru uku.

Dubban mutanen Afrika ta tsakiya sun fice saboda rikicin kasar
Dubban mutanen Afrika ta tsakiya sun fice saboda rikicin kasar REUTERS/Siegfried Modola
Talla

Hukumomin FAO da WFP na samar da tallafin abinci a Majalisar Dinkin Duniya ne suka yi wannan gargadin a rahoton da suka fitar a yau Talata.

Hukumomin biyu sun ce adadin abincin da ake nomawa a kasar ya ragu, tun juyin mulkin watan Maris na 2013 da aka yi wanda ya jefa kasar  cikin rikici.

Al’ummar kasar na cikin hali na rashin abinci kamar yadda Bienvenu Djossa daraktan hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ya bayyana.

Rikikin Afrika ta tsakiya ya sa miliyoyan mutanen kasar ficewa kasar wadanda yawancinsu manoma ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.