Isa ga babban shafi
Senegal

Sall na Senegal zai cika wa'adin shekara 7

Shugaban Senegal Macky Sall, zai ci gaba da rike mukaminsa har zuwa shekara ta 2019 sakamakon hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke, wanda ya bukaci shugaban da ya cike shekaru 7 da aka zabe shi a maimakon yadda ya ke son sauka bayan ya cika shekaru biyar kan karagar mulki.

Shugaban kasar senegal Macky Sall.
Shugaban kasar senegal Macky Sall. AFP PHOTO / THOMAS SAMSON
Talla

A jawabin da ya gabatarwa al’ummar kasar a cikin daren da ya gabata, shugaba Macky Sall, ya ce zai mutunta hukuncin kotun tsarin mulkin, wadda ta ce ala dole sai ya cika shekara 7 saboda akan wannan wa’adin ne al’umma ta zabe shi amma ba shekara biyar ba.

Sai dai duk da cewa shugaba Sall, ya amince ya rike matsayinsa har zuwa shekara ta 2019, to amma ya bayyana 20 ga watan Maris mai zuwa a matsayin ranar da za a gudanar da kuri’ar raba gardama a game da yi wa kudin tsarin mulkin kasar gyaran fuska domin rage yawan shekarun da shugaba zai share akan karagar mulki nan gaba.

An dai zabi Macky Sall ne a shekara ta 2012 domin tafiyar da mulki na tsawon shekara 7, to sai dai a shekarar da ta gabata ya bayyana aniyarsa ta rage wa’adin mulkin zuwa shekara 5, matakin da wasu daga cikin magoya bayansa da kuma ‘yan hamayyarsa suka nuna rashin amincewarsu da shi.

A yanzu dai ko da jama'ar kasar sun amince da yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara domin rage yawan shekarun, dole ne shugaba Sall ya ci gaba da rike matsayinsa har zuwa shekara ta 2019.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.