Macky Sall ne sabon shugaban ECOWAS
Shugabannin kungiyar gamayyar tattalin arzikin Yammacin Afrika ECOWAS ko CEDEAO, sun zabi shugaban kasar Senegal Macky Sall a matsayin sabon shugaban kungiyar. An zabi Shugaba Sall ne a taron da shugabannin kungiyar suka gudanar a birnin Accra na kasar Ghana.
Wallafawa ranar:
Macky Sally a karbi ragamar shugabancin ECOWAS ne daga hannun shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, karkashin tsarin kungiyar na karba-karba.
Shugabannin sun yaba wa Shugaban Najeriya mai jiran gado Goodluck Jonathan bayan ya amince da shan kaye a zaben kasar da aka gudanar a watan Maris.
Kungiyar ECOWAS ta ce dattakun da Goodluck Jonathan ya nuna a Najeriya, ya tabbatar da ci gaban dimokuradiya a Nahiyar Afrika.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu