Taron shugabannin ECOWAS a Ghana
Shubannin Kasashen yammacin Afrika zasu yi wani taro gaggawa a kasar Ghana, karkashin kungiyar hadin kan yankin, ta ECOWAS ko CEDEAO, domin tattauna matsalar tsaron Yankunansu musamman barazanar ayyukan ta’addanci a Mali da Najeriya.
Wallafawa ranar:
Wannan shi ne karon farko da shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama zai karbi bakuncin taron, tun lakacin da aka zabe shi shugaban Majalisar shugabannin na ECOWAS a watan Fabrairun bana.
A Shekarar 2012 kasar Mali ta tsunduma cikin rikici, lokacin da ‘Yan tawayen Abzinawa, suka tayar da kayar baya a arewacin kasar, yayin da kuma hankulan duniya suka koma Najeriya, bayan da Mayakan kungiyar Boko Haram sun yi awon gaba da wasu ‘yan mata sama da 200 a watan Afrilu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu