Isa ga babban shafi
Burundi

'Yan sandan Burundi sun kama 'yan jaridar Birtaniya da Faransa

Jami’an ‘yan sandan kasar Burundi sun cafke ‘yan jaridar Birtaniya da Faransa guda biyu bayan sun kai samame a wasu yankunan kasar da nufin kama ‘yan tawaye kamar yadda hukumomin kasar suka sanar a yau jumma’a. 

Dan jaridar Faransa Jean-Philippe Rémy da takwaransa na Birtaniya  Phil Moore.
Dan jaridar Faransa Jean-Philippe Rémy da takwaransa na Birtaniya Phil Moore. CHARLY TRIBALLEAU, PHIL MOORE / AFP
Talla

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Burundi, Moise Nkurunziza ya ce, an kama dan jaridar Birtaniya Phil Moore da kuma na Faransa Jean Philippe Remy a ranar Alhamis bayan kaddamar da samamen a yankunan Jabe da Nyakabiga da ke kusa da babban birnin Bujumbura.

To sai dai ana ganin wannan al’amari zai haifar da tankiya tsakanin Burundi da masu tallafa mata daga kasashen yamma.

‘Yan jaridar dai na da takardar izinin gudanar da aikin jarida a birnin Bujumbura yayin da ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya bukaci a gaggauta sakin su, inda kuma ofishin jakadancin Birtaniya ya ce, yana nazari akan rahoton kamen.

Tun a watan Aprilun bara ne Burundi ta fada cikin rikici bayan shugaban kasar Pierre Nkurunziza ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takara domin neman wa’adi na uku.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.