Isa ga babban shafi
MDD-Burundi

Rikicin Siyasar Burundi :Jakadun MDD sun isa Kasar

Jakadun Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun isa kasar Burundi, inda za su yi kokarin shawo kan gwamnatin kasar na amincewa da shiga zaman tattaunawa da 'yan adawa.

Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi, Pierre Nkurunziza AFP PHOTO / LANDRY NSHIMIYE
Talla

Wannan dai ita ce ziyara ta 2 da jakadun 15 na Majalisar Dinkin Duniya suka kai a wannan ‘yar karamar kasa, da tun cikin watan Avrilun 2015 da ta gabata ta fada a cikin kazamin rikicin siyasa da ke gab da jefa ta a cikin yakin basasa.

Jakadiyar kasar Amurka Samantha Power ta shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP cewa, suna da hujjar nuna damuwa da abubuwan da suke gani suna wakana a kasar Burundi, inda a ko wane lokaci ake kai hare-hare da gurneti, tare da ganin gawarwakin mutane a kan tituna a duk safiyar Allah.

Jakadiyar ta Amurka Samantha Power ta ce tarihi ya nuna cewa, hasken walkiya na tada belin wutar da nan take zata iya bazuwa ta game ko’ina da sauri.

Kawo yanzu dai tashin hankalin da ke wakana a kasar ta Burundi ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 400 a yayinda ya tilastawa wasu dubu 200 barin gidajensu a cewar MDD.

Jakadun dai za suyi kokari gani cewa Gwamnatin kasar ta amince da tura dakarun rundunar samar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika a kasar.

Burundi dai a baya ta taba fadawa a cikin yakin basasar da ya yi sanadiyar rasa rayukan dubban mutane a tsakanin 1993 da 2006.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.