Isa ga babban shafi
Afrika

Afrika na fama da karancin abinci- FAO

Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, ta ce kasashen yankin kudancin Afirka na fama da karancin abinci sakamakon matsalar sauyin yanayi da ake kira El Nino wadda ta shafi yankin.

Matsalar karancin abincin ta fi shafar manoma masara.
Matsalar karancin abincin ta fi shafar manoma masara. AFP PHOTO/SIMON MAINA
Talla

Hukumar ta FOA ta ce matsalar canjin yanayi ta El Nino ta haddasa fari wanda kuma ya shafi aikin noma a kasashen yankin na kudancin Afirka baki daya.

Hukumar ta ce matsalar ta soma bayyana ne a cikin watannin da suka gabata a yankin, kuma hasashen masana ya gano cewa za ta ci gaba da faruwa har zuwa shekarar badi, kuma a irin wannan yanayi akwai bukatar kasashen yankin su dauki matakan gaggawa domin tunkarar barazanar karancin abinci.

Matsalar dai ta fi shafar manoma masara, wanda shi ne nau’in abinci da aka fi nomawa a yankin, kuma a cewar FAO, matsalar za ta shafi kusan kashi 80 cikin 100 na amfanin gonar da aka girbe a kakar bana, yayin da manoman suka yi asarar kusan kashi 27 cikin 100 na abinda suka saba girbewa a shekara.

El Nino dai wata matsala ce da masana ke cewa tana da nasaba da dumamar yanayi, wadda a yau ta shafi illahirin kasashen kudancin Afirka wadanda ke gabar teku.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.