Isa ga babban shafi
Congo

Fada ya kazance tsakanin Soji da ‘yan tawayen Uganda a Congo

Fada tsakanin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya da ‘yan tawayen Uganda ya kazance bayan martanin da dakarun suka mayar a kan ‘yan tawayen, sanadiyar harin da ‘yan tawayen suka kai da ya hallaka mutane 24 a karshen mako.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Rahotanni yanzu na cewa ‘yan tawayen sun dai janye bayan kwashe tsawon awanni ana fafatawa dasu a yankin Kivu da ke yammancin Demokradiyar Congo.

Ana dai zargin ‘Yan tawayen Uganda da laifin kashe mutane akalla sama da dari hudu da hamsin daga shekara ta 2014 zuwa yanzu, yawanci mamatan kuma farrren hula ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.