Isa ga babban shafi
Afrika

An samu nasara a yaki da cutar sankarau a Afrika

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa an kusa kawar da cutar sankarau a kasashen Afrika amma ta gargadi cewa cutar na iya dawo wa muddin kasashen suka kauce wa ci gaba da karbar sabon allurar riga-kafin cutar akai akai.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce an samu gagarumar nasara wajan kawar da cutar sankarau a Afrika.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce an samu gagarumar nasara wajan kawar da cutar sankarau a Afrika. meningvax.org
Talla

kimanin shekaru biyar kenan da aka fara wayar da kan jama’a dangane da karbar allurar riga-kafin cutar da ake kira MenAfricVac a kasashen Afrika da suka fi fama da cutar ta sankarau wadda ta yadu daga Senegal da Habasha zuwa sauran nahiyar.

Hukumar lafiyar ta ce an samu gagarumar nasara wajan yaki da cutar amma da yiwuar cutar ta kara tsananta nanda shekara ta 2030 matukar an dakatar da karbar allurar riga-kafin.

An samar da samfurin allurar riga-kafin ta MenAfricVac ne bayan ministocin lafiya na kasashen Afrika sun bukamci haka a lokacin da cutar ta barke a shekara ta 1996, inda ta kama sama da mutane dubu 250 baya ga hallaka mutane sama da dubu 25 a cikin watanni kalilan.

Tun daga shekara ta 2010, an yi nasarar yi wa mutane sama da miliyan 237 allurar a kasashe 16 cikin 26 da ke fama da cutar.

A shekara ta 2013 an samu mutane hudu kacal dauke da cutar ta sankarau a daukacin kasashe 26 da ke fama da ita.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.