Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Namun daji:'Yan Sandan Zimbabwe sun gurfanar da 'yan jarida

‘Yan Sanda a Zimbabwe sun gurfanar da wasu ‘yan Jaridan kasar biyu a kotu saboda labarin da suka fitar na cewa ‘yan Sandan da jami’an kula da gandun dajin kasar na da hannu wajen bai wa giwaye sama da 60 guba a watannin da suka wuce.

Amnesty ta yi Allah-wadai da kama 'yan jaridan.
Amnesty ta yi Allah-wadai da kama 'yan jaridan. DR
Talla

‘Yan Sandan sun gurfanar da Mabasa Sasa, Editan Jaridar Sunday Mail, da Editan bincike Brian Chitemba da wakilinsu Tinashe Farawo inda aka zarge su da bada labaran karya wanda ke dauke da hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari.

Rahotan ya yi zargin cewar an samu hadin baki ne tsakanin kwamishinan ‘yan Sanda da jami’an gandun daji da kuma wani dan kasuwa daga nahiyar Asia da ke safarar hauren giwan.

Tuni kungiyar kare hakkin bil-adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da kama ‘yan jaridan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.