Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba za a karya darajar Naira ba

Fadar gwmanatin Najeriya ta ce ba za a karya darajar takardar kudin kasar ta Naira ba a daidai lokacin da masana ke gargadin cewa kin daukar wannan mataki zai iya kara jefa tattalin arzikin a cikin matsala. 

tsabar kudin Najeriya
tsabar kudin Najeriya Juguda.com
Talla

Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo, wanda ke ganawa da jakadojin Italiya da Canada a birnin Abuja jiya alhamis, ya ce domin magance matsalar tattalin arzikin, yanzu haka gwamnati ta tsara wani shiri da zumma sake gina kasar da zai ci dala Bilyan 25.

A watan nuwambar bara ne dai gwamnatin da ta gabata ta karya darajar kudin kasar daga Naira 168 zuwa 198 a matsayin dala daya, yayin da ake sayar da ita a kasuwannin bayan fage akan Naira 222.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.