Isa ga babban shafi
CAF

Najeriya ta tsallake zuwa gasar Afrika a Rwanda

Najeriya ta tsallake zuwa gasar Afrika ta matasa da ke taka kwallo a gida da za a gudanar a Rwanda a badi, bayan ta rike Burkina Faso babu ci a Ouagadougou.

'Yan wasan Najeriya na fafatawa da Ghana
'Yan wasan Najeriya na fafatawa da Ghana CAF
Talla

Najeriya ta samu nasarar tsallakewa ne saboda nasarar kwallaye biyu ta zira a ragar Burkina a karawa ta farko.

Kasashen da suka tsallake gasar sun hada da Rwanda mai masaukin baki da Morocco da Tunisia da Mali da Guinea da Nijar da Gabon da Jamhuriyyar Congo da Uganda da Habasha da Zimbabwe da Zambia da kuma Angola.

A 16 ga watan Janairun 2016 ne za a fara bude gasar a kuma a 7 ga watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.