Isa ga babban shafi
Najeriya-Ghana

Najeriya da Ghana sun Cimma Yarjejeniyar Iskar Gas

Kamfanin Man Feturin Najeriya wato NNPC ya sanar da warware takaddamar da ke akwai tsakanin sa da Gwamnatin Ghana a kan batun dimbin bashi kudin iskar Gas tsakanin kasashen biyu.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Ghana John Mahama.
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Ghana John Mahama. bellanaija.com
Talla

Cimma wannan Matsaya na zuwa ne bayyan wata tattaunawa tsakanin shugaban Ghana, John Dramani Mahama da shugaban NNPC, Ibe Kachukwu da kuma ministan makamashin Ghana, Kwabena Donkor.

Mr. Ibe ya ce a yanzu sun warware batu gas da Hukumar Volta River da ke Ghana, da ya kai na kudin Najeriya sama da Naira biliyan 33, bashin da a baya ya sa kasar ta yi barazanar rage yawan gas din da take tura wa Ghana idan ba ta biya bashin dake kan ta ba.

Najeriya ce ke dawainiyar samarwa Ghana iskar gas da kasar ke bukata domin bunkasa samar da lantarki a kasar.

Rahotanni sun ce a 'yan kwanakin nan, Gwamnatin Ghana na fuskantar Soka sakamakon fama da matsalar karancin wutar lantarki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.