Isa ga babban shafi
Ghana

Ghana na shirin amfani da nukiliya don samar da wutar lantarki

Gwamnatin kasar Ghana ta shiga nazarin soma yin amfani da makamashin nukliya domin wadata kasar da wutar lantarki, sakamakon yadda bukatar wuta ke ci gaba da karuwa a kasar.

John Dramani Mahama, shugaban kasar Ghana
John Dramani Mahama, shugaban kasar Ghana REUTERS/Luc Gnago
Talla

Ghana dai na a matsayin kasar da ke samun habakar tattalin arziki a yammacin Afirka, kuma shugaban kasar John Dramani Mahama na ci gaba da aiwatar da sauye-sauye domin kara bai wa kasar damar kasancewa mai fada a ji a Afirka, lamarin da ya sa har kullum ake samun karuwar bukatar makamashin a kodayaushe.

To sai dai da dama daga cikin al’ummar kasar na nuna shakkunsu a game da hatsarin da ke yin amfani da makamashin nukilya, sakamakon yadda haka ke bukatar daukar matakan tsaro.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.