Isa ga babban shafi
Chadi

Hafsoshin Sojin kasashen Tafkin Chadi na taro a N’Djamena

Manyan hafsoshin sojin kasashen Chadi da Kamaru da Nijar da kuma Najeriya, na gudanar da wani taro a birnin Ndjamena na kasar Chadi, a ci gaba da tsara ayyukan rundunar hadin-gwiwa ta kasa da kasa da aka kafa domin yaki da mayakan Boko Haram da ke ci gaba da zama barazana ga kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi.

Rundunar Soji Chadi da ke yaki da Boko Haram na Najeriya
Rundunar Soji Chadi da ke yaki da Boko Haram na Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Taron wanda aka fara a jiya Alhamis, shi ne irinsa na farko tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ziyarci kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da kuma Benin, bayan zabensa a matsayin shugaba.

Kafin nan dai gwamnatin Kamaru da kuma Benin, sun sanar da adadin dakarun da suke shirin bai wa rundunar ta kasa ta kasa domin yaki da Boko Haram.

Rundunar ta kasashe biyar ta kunshi dakaru 8,700 da za su kaddamar da yaki gadan-gadan da Mayakan Boko Haram.

Buhari ya ba rundunar Sojin Najeriya wa’adin watanni uku ta murkushe Boko Haram.

Taron na zuwa ne a yayin da Shugaban Boko Haram Abubakar shekau ya aiko da sakon sauti, yana karyata ikirarin Shugaban Chadi Idriss Deby game da nada Muhammad Dawud a matsayin sabon jagoran Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.