Isa ga babban shafi
Nijar

Mutane 9 sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a Nijar

Hukumomi a Jamhuriyar sun tabbatar da mutuwar mutane 9 sakamakon kifewar wani kwale-kwale a yankin Tillabery da ke yammacin kasar.

Kogin Niger
Kogin Niger AFP PHOTO / OXFAM
Talla

Gidan rediyon gwamnatin kasar Voix du Sahel ya ce mutanen tara sun hallaka ne a lokacin da suke kokarin tsallaka kogin Niger ko kuma Isa kamar yadda ake kiran sa domin zuwa gona.

Daga cikin wadanda suka mutu akwai mata shida, wani matashi dan makarantar sakandare, jinjiri dan watanni shida da kuma matukin kwale-kwalen. Hukumomin sun ce cikar kogin ce ta haddasa wannan hatsari.

A lokacin da lamarin ya faru, akwai mutane 11 ne a cikin wannan kwale-kwale.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.