Isa ga babban shafi
Masar

Sisi ya sanya hannu kan dokar ta’addanci a Masar

Shugaban Kasar Masar Abdel Fatah al Sisi ya sanya hannu kan wata sabuwar dokar yaki da ta’addanci da ta kunshi hukunci mai tsanani da kuma dakatar da mai laifi daga wurin aiki saboda bayar da labarin da ya sabawa gwamnati game da harin ta’addanci.

Shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi
Shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Dokar ta kuma kunshi tarar Dala 25,000 kan duk wanda ya wallafa labarin da ba shi da gaskiya kan harin da ake kai wa jami’an tsaro, tare da rufe kafofin yada labarai da suka watsa labarin alkalumman da suka sabawa na gwamnati

Wannan doka ta biyo bayan rahotan cewar Yan Tawaye sun kashe sojoji da dama maimakon 21 da hukumomi suka sanar a harin Sinai.

Majalisar Masar ta yi wa dokar yaki da ta’addancin kwaskwarima, inda aka sauya hukunci dauri akan ‘Yan Jarida zuwa Tara idan har suka wallafa labarin alkalumman hare haren ta’addanci da suka sabawa na gwamnatin kasar.

A cewar Kungiyar Amnesty sanya wannan doka ya sabawa ka’idar ‘yanci fadin albarkacin baki, tare da tauye hakkin dan adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.