Isa ga babban shafi
Burundi

Gwamnatin Burundi ta shiga sabon tattaunawa da 'yan adawa

Gwamantin kasar Burundi ta shiga wani sabon tattaunawa da ‘yan adawar Kasar a yau asabar, a wani yunkuri na samar da maslaha dangane da rikicin siyasa da kasar ta tsinci kanta a ciki.

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza AFP PHOTO / MARCO LONGARI
Talla

A ranar talata mai zuwa ne ya kamata a gudanar da zaben shugabacin kasar yayin da a farko ‘yan adawar suka bayyana cewa zasu kauracewa zaben, lamarin da yasa ake neman cimma matsaya da su.

Kawo yanzu dai yan takarar shugabancin kasar uku daga cikin takwas sun janye daga tsayawa takara.

Tun bayan da Shugaban Kasar Pierre Nnkrunziza ya bayyana ayyiyarsa ta sake tsayawa takara a wa’adi na uku Burundi ta tsinci kanta a cikin tashe tashen hankula.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.