Isa ga babban shafi
Algeria- Faransa

Hollande na ziyara a Algeria

Shugaban Faransa Francois Hollande na ziyarar aiki a kasar Algeria domin tattauna matsalolin ‘Yan ta’adda a kasashen Mali da Libya.

Francois Hollande na jawabi ga manema labarai a lokacin da ya isa Algeria.
Francois Hollande na jawabi ga manema labarai a lokacin da ya isa Algeria. REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

Sai dai kuma shugaba Hollande na ziyarar ne , a yayin da al’ummar kasar ke ci gaba da nuna adawa da shugaba Bouteflika wanda aka jima ba a gani ba saboda rashin lafiyar da yak e fama da ita.

Ziyarar shugaban na Faransa na zuwa ne a yayin da gwamnatin Libya ta bayar da sanarwar cewa an kashe Mokhtar Belmokhtar, a wasu hare haren Amurka na jiragen yaki.

Ana sa ran Hollande zai gana da shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika da Firaministan kasar Abdelmalek Sellal.

Sai dai har yanzu al’ummar Algeria na ci gaba da bayyana adawa da shugaba Bouteflika wanda suka dade ba su gani ba saboda rashin lafiya yayainda Faransa ba ta ce uffan ba game da rashin lafiyarsa da magudin da ‘yan kasar ke zargin an tafka a lokacin zabensa wa’adi na hudu.

Kasashen biyu kuma zasu tattauna huldar cinikayya da kasuwanci duk da sabanin da ke tsakaninsu a shekarun baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.