Isa ga babban shafi
MDD

Dakarun MDD na yin lalata da Yara

A wani rahotan da ta fitar Majalisar Dinkin Duniya ta ce, dakarunta da ke aikin wanzar da zaman lafiya suna yin amfani da kudi, da wayoyin Salula da kayan ado har ma da Telebijin domin janyo hankalin ‘Yan mata don su yi lalata da su.

Dakarun Wanzar da Zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya
Dakarun Wanzar da Zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya UN Photo/Myriam Asmani
Talla

Rahoton ya ce Dakarun na bayar da kyautar ne a matsayin tukuicin domin yin lalata da kanana yara a kasashen da aka tura su aiki.

A wani bincike da Majalisar ta gudanar a kasashen Haiti da Liberia, binciken ya gano cewar yawanci dakarunta na yin lalata da yara ‘Yan kasa da shekaru 18.

Rahoton ya bayyana cewa a kasar Haiti akalla mata 231 dakarun suka lalata, inda suke basu kyautar sarkoki da takalma da kayayyakin sawa har da wayoyi da duk wani kayayyakin alatu a matsayin tukuici don su amince da su.

A cewar wannan rahoton yawanci matan da ake amfani da su, mata ne da ke cikin matsananci yunwa, wadanda ke cikin mawuyacin hali ko suka rasa muhallinsu.

Rahoron yace a Liberia kashi 1 cikin 4 na matan kasar wadanda shekarunsu ya fara daga 18-30 na aikata lalata da dakarun saboda talauci.

Akalla dakarun Majalisar Dinkin Duniya 125,000 ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasashen 16.

Sakatare janar na Majalisar Ban-ki moon ya ce za su dauki matakan gagawa akan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.