Isa ga babban shafi
LIBYA-MDD

Majalisar libya ta yi watsi da batun yarjejeniyar zaman lafiya

Majalisar Kasar Libya dake samun goyan bayan kasahsen duniya ta bayyana rashin amincewar ta da yarjejeniyar zaman lafiyar da Majalisar dinkin Duniya ta gabatar, inda ta bukaci wakilan ta dake halartar taron da su dawo gida dan tattaunawa.

Taron Majalisar Dinkin Duniya akan Libya
Taron Majalisar Dinkin Duniya akan Libya Reuters
Talla

Mai Magana da yawun majalisar, Frdaj Abou Hachem, ya ce duk wani wakilin da ya halarci taron da kasashen duniya suka shirya a Berlin yau, ya san cewar ya yi gaban kan sa ne kawai.

Majalisar Dinkin Duniya na cigaba da kokarin ganin bangarorin dake rikici a Libya sun amince da yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kai dan kawo karshen tashin hankalin da ake samu a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.