Isa ga babban shafi
Libya

Shekaru 4 da kaddamar da zanga-zanga a Libya

Shekaru hudu ke nan a yau ranar 17 ga watan Fabrairu da aka kaddamar da zanga-zangar adawa da gwamnatin marigayi Kanal Gaddafi a garin Benghazi na Libya, amma tun bayan kawar da shi har yanzu an kasa samar da zaman lafiya a kasar.

Marigayi Kanal Gaddafi na Libya
Marigayi Kanal Gaddafi na Libya © AFP
Talla

Kungiyar NATO ta shiga riikicin bayan zanga-zangar ta bazu daga Benghazi zuwa sasan kasar Libya.

A ranar 20 ga watan Oktoban 2011 aka kashe Kanal Gaddafi a garin Sirte, bayan dakarun NATO sun taimakawa ‘Yan tawaye.

Tun a lokacin kasar Libya ta fada cikin rudani.

Yanzu haka kungiyar Kasashen Turai ta bukaci daukar matakin gaggawa don ceto kasar Libya daga rugujewa.

Babbar jami’ar diflomasiyar kasashen Turai Federica Mogherini ta ce za ta tattauna da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da takwaransa na Masar Sameh Shoukry a Washington domin samo hanyar da za a shawo kan matsalar tsaron da ta addabi kasar Libya yanzu haka.

Jami’ar ta ce abin da suke gani yau a Libya ya zama barazanar rarrabewar kasar da kuma bai wa ‘yan ta’adda damar karbe ikon kasar.

A shekarun baya matakin soji da majalisar Dinkin Duniya ta bayar da dama ne a karkashin jagorancin kasar Faransa ya kifar da gwamnatin shugaba Muammar Gaddafi.

Tutar Kasar Libya
Tutar Kasar Libya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.