Isa ga babban shafi
Najeriya

Bidiyo: Boko Haram ta karyata ikirarin Sojojin Najeriya na samun nasara

Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo a yau Talata, inda Mayakan ke karyata ikirarin Sojojin Najeriya na samun nasara akansu, amma bidiyon bai nuna hoton shugaban kungiyar Abubakar shekau ba ko wanda ke magana da yawun kungiyar a sakon mai taken "Daular Islama a Afrika".

Tankunan Yaki da Dakarun Najeriya suka kwato daga hannun Mayakan Boko Haram
Tankunan Yaki da Dakarun Najeriya suka kwato daga hannun Mayakan Boko Haram REUTERS
Talla

Mai magana da yawun kungiyar da ba a nuna fuskarsa ba a sakon bidiyon ya kira Najeriya da Kamaru da Chadi da Nijar da ke fada su a matsayin makaryata.

A cikin sakon bidiyon na tsawon minti 10, kungiyar ta ce tana ci gaba samun nasara

Sakon bidiyon na zuwa a yayin da mayakan suka kaddamar da sabbin hare haren kunar bakin wake a Maiduguri.

A yau Talata an kai wani harin kunar bakin wake a wata kasuwar Shanu a garin Maiduguri, kuma ana kyautata tunanin harin ya shafi mutane da dama.

Zuwa yanzu babu bayani akan adadin mutanen da suka mutu.

A ranar Assabar wani dan kunar bakin wake ya dala wa kansa bom a lokacin da mutane ke cikin sallah a wani masallacin Maiduguri inda mutane 26 suka mutu tare da raunana 28.

Yanzu haka sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na kan tattaunawa da manyan jami’an tsaron kasar game da matsalar Boko Haram.

Shugaban wanda ya sha alwashin murkushe ayyukan Boko Haram, ana sa san zai kai ziyara kasashen Nijar da Chadi a cikin makon nan domin tattaunawa da shugabannin kasashen kan Boko Haram.

A cikin jawabinsa na farko a matsayin sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce bayar da umurnin yaki da Boko Haram zai tashi daga Abuja zuwa garin Maiduguri domin kakkabe mayakan. Sannan shugaban ya ce gwamnatinsa za ta yi kokarin ceto ‘Yan Matan garin Chibok da aka sace sama da shekara guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.