Isa ga babban shafi
Nigeria

Mutane 26 ne suka rasu a harin bam da aka kai Maiduguri

Rundunar ‘yan sandar jihar Borno da ke tarayyar Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 26 sakamakon harin bam da aka kai a wani masallaci da ke birnin Maiduguri a jihar asabar.

Wani masallacin 'yan Boko Haram da jami'an tsaro suka kona
Wani masallacin 'yan Boko Haram da jami'an tsaro suka kona AFP
Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya jiyo komishinan ‘yan sandan jihar ta Borno Aderemi Opadokun, na cewa harin ya yi muni matuka, kuma akwai yiyuwar adadin mamatan zai iya karuwa sakamakon munanan raunukan da suka sama.

Kwana daya kafin nan dai wasu da aka ce magoya bayan ‘yan Boko Haram ne sun harba manyan rokoki da suka fada a wasu unguwanni da ke gefen birnin na Maiduguri tare da kashe mutane akalla 8, kuma lamarin na faruwa ne a daidai lokacin da sabon shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi alkawalin mayar da babbar cibiyar gudanarwa ta aikin soja zuwa Maiduguri fadar gwamnatin Borno, domin kara daura damara wajen fada da mayakan wannan kungiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.