Isa ga babban shafi
Ebola

Wani kwararre yace mai yuwuwa cutar Ebola ta sake bayyana a duniya

Wani kwararren masani kan harkokin kula fa lafiya dan kasar Congo, Jean-Jacques Muyembe yayi gargadin cewa akwai yuwuwar cutar Ebola mai saurin kisa, zata sake far wa al’ummar duniya. Muyembe, wanda ke daya daga cikin masu bincike kan cutar ta Ebola, tun lokacin da aka fara gano ta a shekarar 1976, yayi gargadin cewa in Ebola tazo a wannan karon duk duniya zata yi ta’adi.Cutar Ebola, da zuwa yanzu aka shawo kanta, tayi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane dubu 11 a kasashen Liberia, Saliyo da Guinea, tun lokacin data bayyana a baya bayan nan. 

Jami'an kula da lafiya masu yaki da cutar Ebola
Jami'an kula da lafiya masu yaki da cutar Ebola REUTERS/Daniel Berehulak/The New York Times/
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.