Isa ga babban shafi
Ebola

Ebola: Amurka na sa ido kan 'yan kasarta da aka mayar daga kasar Saliyo

Hukumomin kasar Amurka sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike kan ma’aikatan lafiya 10 da aka koma gida dasu daga kasar Saliyo, saboda mu’ammala da masu fama da cutar Ebola.Cibiyar hanna yaduwar cuttutuka dake Amurka CDC ta ce dawo da ma’aikatan 10 masu bada agaji a Saliyo ya biyo bayan samun wani Ma’aikacin su guda dake dauke da cutar, wanda shima tuni aka mayar dashi wani babban asibiti a Washington don karba magani.Cibiyar ta kuma kara da cewa 10 da aka kwashe a yanzu ana zargin sunyi mu’amala da dashi, don haka ya zama dole a kebe su don tabbatar da cewa suma basu yadda cutar ba kamar yadda mai Magana a madadin kungiyar Kathy Harben ta shaidawa kamfanin dilanci labaran fransa AFP.Kathy ta ce har yanzu dai babu wanda aka samu dauke da cutar acikin su, amma duk da haka za’a cigaba da sa musu ido har na tsahon kwanaki 21, kana duk wanda alamomi suka nuna yana dauke da cutar za’a gaugauta aiki shi zuwa babba asibitin su, don samun magani.  

Shugaban Amurka Barak Obama, yana magana kan ci gaban da aka samu a yaki da cutar Ebola
Shugaban Amurka Barak Obama, yana magana kan ci gaban da aka samu a yaki da cutar Ebola REUTERS/Jonathan Ernst
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.