Isa ga babban shafi
Sudan

Al Bashir ya lashe zaben Sudan

Hukumar zaben Sudan tace Omar Hassan al Bashir ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar da kusan kashi 94, inda zai sake shafe wasu shekaru biyar yana jagorantar kasar. Jam’iyyar Al Bashir kuma ta lashe kujerun ‘Yan majalisa da gagarumin rinjaye, ko da ya ke ‘yan adawa sun kauracewa zaben.

Omar Hassan al-Bashir zai sake shafe shekaru 5 yana shugabanci a Sudan
Omar Hassan al-Bashir zai sake shafe shekaru 5 yana shugabanci a Sudan REUTERS
Talla

Al Bashir ya sake lashe zaben Sudan duk da zarginsa da kotun ICC ke yi da aikata laifukan yaki, yayin da kuma ya ke ci gaba da fuskantar suka daga kasashen yammaci.

‘Yan takara uku ne suka fafata da Al Bashir a zaben bayan manyan ‘yan adawar kasar sun kaurace.

A lokacin da ya ke sanar da sakamakon zaben, Shugaban hukumar zaben kasar Mukhtar Al Asam ya ce al Bashir ya samu kuri’u fiye da kashi 94, kuma jam’iyarsa ta NCP ta lashe kujerun Majalisa 323 cikin 426.

Kasashen yammaci da dama dai sun soki zaben, musamman kungiyar Tarayyar Turai da Amurka da Birtaniya da Norway.

Amma masu sharhi na ganin mutanen Sudan sun gamsu da shugabancin al Bashir shi ya sanya suka sake zabensa duk da wasu ‘Yan adawa sun kauracewa zaben.

"Zaben ya nuna cewar mai daki shi ya san inda ya ke ma sa yoyo" a cewar Ahmed Tijjani Lawal mai sharhi kan lamurran kasashen larabawa.

Al Bashir dai ya dare kan karagar mulki ne ta hanyar juyin mulki a 1989, kuma a zamaninsa ne Sudan ta kudu ta balle daga kasar.

Kalubalen da ke gaban al Bashir a yanzu shi ne farfado da tattalin arzikin kasar tare da kawo karshen rikici a yankin Darfur da Blue Nile da kudancin Kordufan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.