Isa ga babban shafi
Ghana-Cote D'ivoire

Kotun ta umurci kasar Ghana da ta daina hako mai

Wata Kotun duniya ta baiwa kasar Ghana umurnin daina hako mai a cikin tekun da suke takaddama da kasar Cote d’Ivoire har sai ta kamala shari’ar dake tsakanin kasashen biyu. 

Mayan biranen Abidjan na Cote D'Ivoire da Accra dake Ghana
Mayan biranen Abidjan na Cote D'Ivoire da Accra dake Ghana Photo:Montage/RFI
Talla

Kasar Cote d’Ivoire ne ta ruga kotun dan ganin an bi mata kadi a takaddamar da take da Ghana dan mutunta dokar hakar mai a ruwa.
Gwamnatin kasar ta bukaci kotun dake Hamburg  na kasar Jamus da ta dakatar da duk wani aikin hako man da Ghana keyi har sai an kamala shari’ar.

Kasashen biyu dai na rikici kan iyakar da ta hada su kuma nan ne aka samu mai a cikin teku, wanda tuni kasar Ghana ta fara hako shi.
Kokarin sasantawa tsakanin kasahsen ya citura abinda ya sa Cote d’Ivoire ta kai kara kotun dan warware matsalar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.