Isa ga babban shafi
Nijar

Cutar Sankarau ta kashe mutane 129 a Nijar

Hukumomin Jamhuriyyar Nijar sun ce cutar Sankarau ta kashe mutane 129 tun a watan Janairu, a yayin da aka soma rigakafin cutar a Makarantun Firamaren Yamai da Jihar Dosso a yau Juma’a. A cewar Ma'aikatar lafiya kimanin mutane 1,150 suka kamu da cutar ta Sankarau.

meningvax.org
Talla

Ministan kiwon lafiya Mano Aghali ya ce cutar na ci gaba da karuwa kuma za a soma rigakafin ne yau Juma’a, a makarantun Firamare.

A cewar Ministan kimanin mutane 1,150 suka kamu da cutar ta Sankarau.

Ministan ya ce tuni maganin Rigakafin ya iso Yamai babban birnin Jamhuriyyar Nijar, kuma suna fatar samun kawar da cutar a kasar.

Cutar Sankarau dai ta shafi Jihohin Nijar kusan guda 7, kamar yadda ministan ya tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.