Sarkin Zulu ya musanta zargin hura wutar kyamar baki
Sarkin Zulu da ke kasar Afirka ta kudu, Goodwill Zwelithini ya nesanta kansa da zargin tinzira al’ummar kasar su afkawa baki wajen kai musu hare hare, bayan zarginsa da hura wutar rikicin da ya janyo hasarar rayukan akalla mutane bakwai.
Wallafawa ranar:
Sarkin da ke jawabi ga dubban ‘yan kabilarsa a Durban, ya ce zargin da ya yi wa ‘yan kasashen waje kan matsalar da ake samu na tsaro a cikin kasar bai da nasaba da kai musu hari.
Sarkin ya ce ya yi kira ne ga ‘Yan sanda su inganta aikin tsaro.
Kasashe da dama dai sun yi allawadai da hare haren da mutanen Afrika ta kudu ke kai wa baki ‘yan kasashen waje.
Yanzu haka an cafke mutane sama da 300 bayan mutuwar mutane 7 a hare haren da ‘yan kasar suka kai wa baki da kasuwanci a Johannesburg.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu