Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Afrika ta kudu ta yi tir da harin da ake kaiwa baki a Kasar

Hukumomin kasar Africa ta kudu sun yi Allah wadai da hare haren da ake kaiwa ‘yan kasashen waje a cikin kasar

Shugaban Kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma
Shugaban Kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Shugaba Jacob Zuma ya nemi ‘yan kasar su gaggauta dakatar da hare haren da suke kaiwa bakin.

A wani taron maneme labarai ,Zuma ya ce babu wata matsalar tattalin arziki ko rashin gamsuwa da za ta halattawa mutane kai hari ga ‘yan kasashen waje, kuma ya yi kira ga jama’ar kasar da su mutunta duk wani bako da ya shigo kasar Afrika ta kudu bisa doka.

Kimanin bakin kasashen ketare dubu daya ne suka kauracewa gidajensu a Afrika ta kudu sakamakon farmakin da ‘yan asalin kasar ke kaddamar masu, inda su ke zargin su da mamaye guraben ayyukan yi a kasar.

Jami’an ‘yan sanda ne suka baiwa bakin mafaka a ofisoshin ‘yan sanda.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.