Isa ga babban shafi
Nijar-Chadi

Dakarun Chadi sun kashe ‘Yan Boko Haram da dama

Rundunar sojin kasar Chadi ta ce dakarunta sun kashe mayakan Boko Haram da dama a musayar wutar da suka yi a garin Malam Fatori da suka kwato, amma Sojojin kasar 9 suka mutu.Kakakin rundunar Sojin Chadi Azam Bermandoa ya ce an kashe sojojinsu 9 yayin da 16 suka samu rauni amma sun kashe daruruwan ‘Yan Boko Haram.

Garin Damasak da dakarun Chadi da Nijar suka kwato daga hannun Boko Haram
Garin Damasak da dakarun Chadi da Nijar suka kwato daga hannun Boko Haram REUTERS
Talla

Dakarun Chadi da Nijar sun fatattaki Boko Haram a Malam Fatori da ke kan iyaka da Nijar, kuma Bermandoa ya ce sojojin sun kakkabe Boko Haram.

A watan Nuwamba ne Boko Haram ta kwace Malam Fatori, bayan ta yi ikirarin kafa sabuwar daula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.