Isa ga babban shafi
Tanzania

An kama Matsafa 225 a Tanzania saboda kisan Zabiya

Kimanin matsafa 225 ne aka kama a wani samame da jami’an ‘Yan Sandan Tanzania suka kaddamar, sakamakon zarginsu da laifin kashe Zabiya dan amfani da su wajan tsafe tsafe

Talla

Jami’an ‘Yan Sandan sun kame Bokayen da basu mallaki lasisi ba, kuma suke aikin bada magungunan gargajiya a kasar.

Mai magana da yawun ‘Yan Sanda, Advera Bulimba, ya bayyana cewa, sun samu wasu kayayyaki  daga  wajan Bokayen, da suka hada da fatar kadangare, hakoran aladu, kwan jimina, bindin biri, kafar tsutsuwa, bindin jaki da fatar zaki.

Bulimba ya jaddada kudirinsu na yaki da Matsafa da ‘Yan kasuwan dake siyar masu da kayayyakin tsafin.

Samamen dai na zuwa ne, kwanaki kadan, bayan shugaban kasar Jakaya Kikwete, ya  yi Allah wadai bisa cigaba da kamun da ake yiwa Zabiya, inda ake amfani da sassan jikinsu domin tsafi.

Tun shekara ta 2000, an kashe kimanin Zabiya 76 bayan cire sassan jikinsu da ake siyarwa a kan dala dari 6, yayinda kuma, ake siyar da dukkan gangan jikin, akan dalar dubu 75.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.