Isa ga babban shafi
Najeriya

MEND tana goyon bayan Buhari

Kungiyar MEND da ke ikrarin fafutukar ‘Yantar da Yankin Naija Delta ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana goyan bayanta ga Dan takarar Jam’iyyar APC, tosohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari.

Tsohon Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari
Tsohon Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari Reuters
Talla

A cikin sanarwar mai dauke dauke da sa hannu Jomo Gbomo da Rediyo Faransa ya samu kwafi Kungiyar tace bayan nazarin halin da Najeriya ke ciki, ta bayyana goyan bayanta ga Dan takaran Jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari don ceto kasar daga cikin halin da ta samu kanta.

Kungiyar ta bayyana korafe korafenta kan rashin yaki da cin hanci da rashawa, inda ta yaba da shirin Buhari na soke Ofishin matar shugaban kasa, da kuma lura da yadda tsananin talauci ya yi wa Yankin Naija Delta katutu da kuma gurbata muhalli da kamfanonin mai ke yi.

Kungiyar ta kuma yi tsokaci kan yadda ake satar mai a Yankin inda ta ke zargin wasu manyan hafsoshin sojin kasar da hannu ciki tare da jami’an gwamnatin kasar.

Kungiyar tace Yankin Naija Delta da ke da ma’aikata tare da hukumar NDDC da hukumar da ke kula da ahuwa da kuma makudan kudin da ake ware ma sa a matsayin kaso na musamman don samar da ci gaba ya zama abin dariya saboda babu wani abin da zaa iya nunawa a gani, dalilin da ya sa suke bukatar canji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.