Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta ce tana da kayan fadan da za ta tunkari Boko Haram

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yi ikrarin cewar tana da kayan fada da ‘ya’yan kungiyar Boko Haram da suka addabi yankin Arewacin kasar.

Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan
Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Ikrarin na hukumomin tarayyar Najeriyar dai ya zo ne a dai dai lokacin da daukacin al’ummar kasar suka kosa da yawan fitar da labarai marasa dadi na hare-haren ‘ya’yan kungiyar Boko Haram, ba tare da suna ganin matakan da hukumomin kasar ke dauka don dakushe kungiyar na yin wani tasiri ba.

Masu lura da lamurran tsaron kasar na ganin cewar ya kamata gwamnatin ta maida himma ga aikin da ke gabanta, maimakon fito da bayannai kadai.

A wani taron manema labarai da ya gabatar, Shugaban hukumar wayar da kan al’uma ta NOA, Mike Omeri ya ce ba gaskiya ba ne yanda ake ta kururuta cewar Boko Haram sun fi sojin gwamnati kayan fada.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.