Isa ga babban shafi
Nigeria

Akalla mutane 15 ne suka mutu sakamakon tashin bam a Maiduguri

Rahotanni daga birnin Maiduguri na tarayyar Najeriya, sun ce wani abu da ake zaton cewa bam ne da aka boye a cikin wata mota da ke dauke da gawayi, ya fashe a kusa da kasuwar birnin da misalin karfe 8 da mintuna 20 na safiyar yau talata.

Harin bam da a garin Maiduguri Najeriya
Harin bam da a garin Maiduguri Najeriya (Photo : Reuters)
Talla

Bayanai na nuni da cewa lamarin ya faru ne a kusa da ginin hukumar samar da wutar lantarki ta kasa wato PHCN da ke gefen kasuwar, kuma mafi yawa daga cikin wadanda ke gudanar da sana'o'insu a wajen tsofaffi ne da ke sayar da gyada da goro da kuma mabarata.

Rundunar tsaron kasar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce wani abu ne ya fashe a cikin motar da ke dauke da gawayi, yayin da wasu rahotanni ke cewa wasu matasa da suka harzuka, sun yi yunkurin afkawa jami'an kwana-kwana da aka tura zura inda lamarin ya faru, bisa zargin cewa jami'an sun zo a makare.

Kawo yanzu dai hukumomin tsaro ba su bayyana adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon harin ba, yayin da tuni aka soma danganta hakan da kungiyar Boko Haram wadda sau da dama ta dauki alhakin hare-haren da ake kai wa yankin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.