Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Kungiyar likitoci ta koka kan yadda ake kashe fararen hula a Sudan ta Kudu

Wani rahoto da kungiyar bayar da agaji ta Medecins Sans Frontieres ta fitar, ya bayyana cewa ana kashe fararen hula da dama a kowace rana a kasar Sudan ta Kudu mai fama da yakin basasa.

Dakarun Sudan ta Kudu loakcin da suke sintiri akan titi
Dakarun Sudan ta Kudu loakcin da suke sintiri akan titi REUTERS/Andreea Campeanu
Talla

Shugaban ofishin kungiyar a kasar, Raphael Gorgeu, ya ce ‘yan bindiga na kai wa fararen hula hari akai akai, kuma a wasu lokuta ana kai hare-haren ne a cikin asibitoci, inda ake kashe harda marasa lafiya da ke kwance a gadon asibiti.

Har ila yau babban jami’in na Medecins Sans frontiers ya ce sau da dama maharan na kona asibitoci da kuma sauran kayan aiki da jami’an kiwon lafiya ke amfani da su domin kulawa da jama’a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.