Isa ga babban shafi
Mauritania

Zaben Shugaban kasa a Mauritania

Al’ummar kasar Mauritania sun jefa kuri’ar zaben shugaban kasa a yau Assabar, zaben da ake ganin babu tantama shugaban kasar mai ci Mohammed Abdel Aziz zai lashe saboda ‘Yan adawa sun kauracewa zaben.

Wata Mata rufe da fuskan tana kada kuri'ar zaben shugaban kasa a Mauritania
Wata Mata rufe da fuskan tana kada kuri'ar zaben shugaban kasa a Mauritania REUTERS/Joe Penney
Talla

Shugaba Abdel Aziz wanda tsohon Janar din Soja ne, a watan Agusta a shekarar 2008 ya dare saman kujerar shugaban kasa ta hanyar juyin mulki.

A yakin neman zabensa, Shugaba Abdel Aziz ya bukaci al’ummar kasar Mauritania su zabe shi saboda irin rawar da ya taka wajen yaki da Mayakan Al Qaeda a kasar da makwabtan kasashe.

Da misalin karfe bakwai na safe ne agogon GMT aka bude runfunan zabe, sai dai kuma rahotanni sun ce an samu karancin masu kada kuri’a saboda ‘Yan adawa sun kauracewa zaben.

Yawancin  mutanen kasar Mauritania musulmi ne, kuma an kwashe lokaci mayakan Al Qaeda a reshen Magrib suna yin garkuwa da mutane a kasar.

Sai dai kuma ‘Yan adawa suna ganin babu wata rawa da Shugaban ya taka wajen magance barazanar tsaro a kasar tare da zargin za’a tafka magudi a zaben

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.