Isa ga babban shafi
Faransa-Najeriya

Shugaba Hollande na jagorantar taro kan batun tsaro a Najeriya

A wannan asabar shugaba Francois Hollande na Faransa na daukar nauyin taron musamman kan matsalar tsaro a tarayyar Najeriya, taron da ke gudana a fadarsa ta Elysees da ke birnin Paris.

Shugaba François Hollande da takwaran aikinsa na Najeriya Goodluck Jonathan a fadar Elysée
Shugaba François Hollande da takwaran aikinsa na Najeriya Goodluck Jonathan a fadar Elysée REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, da takwaransa Issifou Mahamadou na Jamhuriyar Nijar, da Shugaban Chadi Idris Deby Itno, da Charles Bony Yayi na Jamhuriyar Benin, da Paul Biya na Kamaru, yayin da wakilai daga Birtaniya da kuma Kungiyar tarayyar Tuiia duk na halartar wannan taro, da ke duba yiyuwar samar da sabbin dubaru kan yadda za a ceto Najeriya daga matsalar tsaron da take fama da ita sakamakon bullar Kungiyar Boko Haram.

Duk da cewa an share tsawon shekaru 4 kungiyar da kuma jami’an tsaro na kai wa juna hare-hare tare da haddasa asarar rayukan dubban mutane, to amma hankulan kasashen duniya sun dawo kan Najeriya ba sai bayan da Boko Haram ta yi ikirarin sace dalibai mata sama da 200 a garin Chibok na jihar Borno tare da yin barazanar sayar da su a kasuwa da kuma aurar da wasu daga cikinsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.