Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan bindiga sun kai harin bam a Maiduguri

Wasu da ake kyautata zaton Mayakan Kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnah Lid Da'awati wal Jihad ne da ake kira Boko Haram, sun kai harin bam a barikin Sojoji a cikin garin Maduguri. Mazauna garin sun ce ‘Yan bindgar sun yi musayar wuta da Sojoji bayan sun abka cikin Barikinsu.

Wani hari da aka kai a Gidan yarin garin Maiduguri a Jahar Borno
Wani hari da aka kai a Gidan yarin garin Maiduguri a Jahar Borno (Photo : Reuters)
Talla

Wani mazauni garin da ke kusa da Barikin na Soji ya shaidawa RFI Hausa cewa al’amarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a inda suka ji karar fashewar bama bamai da harbin bindiga.

Barikin Sojin dai tana kusa ne da Jami’ar Maiduguri amma babu babu wani bayani akan ko hare haren sun shafi Daliban Jami’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.