Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Mutane 106 suka mutu a hare haren Katsina

Mahukuntan Jahar Katsina a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 106 a hare haren da ‘Yan bindiga suka kai a wasu kauyukan Jahar guda Takwas, kamar yadda Barista Abbas Abdullahi Machika Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar yankunan Kankara da Faskari a Majalisar wakilai ta kasa ya tabbatar.

MD Abubakar Sufeto 'Yan sandan Najeriya
MD Abubakar Sufeto 'Yan sandan Najeriya RFI Hausa
Talla

Amma ‘Yan sandan Jahar sun ce mutane 30 ne suka mutu tare da danganta hare haren ga Fulani makiyaya a Jahar.

Barista Abdullahi yace ‘Yan bindiga sun kai hare haren ne a Kauyukan Jahar Katsina guda Takwas kuma a Marrarabar Maigora an kashe mutane sama da 60.

“Abin da muka tabbatar an kashe mutum 106” a cewar Barista Abbas Abdullahi wanda yace ya kai ziyara a wasu kauyukan.

00:57

Barista Abbas Abdullahi Machika Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar yankunan Kankara da Faskari a Jahar Katsina

Kauyukan da ‘Yan bindiga suka kai hare haren sun hada da Kurar Mota da Unguwar Rimi da sabon Layin Galadima da Dorayi da Fankama da Unguwar Doka da aka kona.

‘Yan sandan Jahar Katsina sun ce hare haren ba su da alaka da Kungiyar Boko haram da ke addabar yankin arewa maso gabacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.