Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta karyata murabus din Aliyu Gusau

Gwamnatin Najeriya ta karyata rahotannin da ke cewa ministan tsaron kasar Janar Aliyu Gusau mai ritaya, ya yi marabus daga kan mukaminsa sakamakon wani sabani da ya shiga tsakanin sabon ministan da kuma manyan hafsoshin sojan kasar.

Ministan tsaro Janar Aliyu Gusau mai ritaya
Ministan tsaro Janar Aliyu Gusau mai ritaya Channelstv
Talla

Kakakin gwamnatin kasar, Dr Reuben Abati, yace ko shakka babu Ministan bai halarci taron Majalisar ministocin kasar da aka gudanar a jiya ba, amma ya sanar da shugaban kasar cewa ba zai samu halartar taron ba saboda wasu dalilai kuma wannan ba ya nufin cewa ya yi marabus.

‘Labarin murabus din Aliyu Gusau ba gaskiya ba ne’ inji Reuben Abati.

Sai dai Rahotanni da ke fitowa daga Najeriya na cewa sabon Ministan na tsaro ya aikawa Goodluck Jonathan da wasika yana mai gargadin yin murabus idan har shugaban bai dauki mataki ba akan manyan hafsoshin Sojan kasar a ma’aikatar tsaro.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.