Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Bauchi ta zartar da hukuncin Bulala ga masu neman maza

Babbar kotun shari’a a garin Bauchi da ke Tarayyar Najeriya a jiya alhamis, ta yanke hukuncin Bulala goma sha biyar biyar a kan wasu mutane hudu tare cinsu tarar kudi Naira 20,000 kowannensu bayan da aka same su da laifin neman maza ‘yan uwansu.

Garin Bauchi a Najeriya
Garin Bauchi a Najeriya AFP/Tony Karumba/File
Talla

Duk da cewa a karkashin tsarin shari’ar musulunci ana iya yankewa mutanen hukuncin kisa, to amma alkalin kotun mai shari’a El-Yakubu Aliyu, ya bayar da umurnin a yi wa mutanen hudu bulala ne, yayin da sauran mutanen hudun da ake tuhuma da aikata irin wannan laifi, za su bayyana a gaban kotun a wata rana nan gaba.

A kwanakin da suka gabata lokacin da aka gabatar da mutane takwas da ake tuhuma a gaban alkali, daruruwan matasa ne suka afkawa kotun inda suke neman a bayar da su domin ladabtar da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.