Isa ga babban shafi
Tunisia

Majalisar Tunisia ta amince da sabon kundin tsarin Mulki

Majalisar Kasar Tunisia ta amince da sabon kundin tsarin mulki, irinsa na farko tun kifar da gwamnatin shugaba Zine el Abidine Ben Ali. ‘Yan Majalisa 200 daga cikin 216 suka amince da sabon kundin, abinda ya nuna fahimtar juna daga bangarorin siyasar kasar.

Mutanen kasar Tunisia inda aka fara kaddamar da zanga-zangar kin jinin gwamnatocin kasashen Larabawa a garin Sidi Bouzid
Mutanen kasar Tunisia inda aka fara kaddamar da zanga-zangar kin jinin gwamnatocin kasashen Larabawa a garin Sidi Bouzid DR
Talla

Sabon kundin tsarin Mulkin dai yana cikin muradun juyin juya halin da al’ummar kasar suka gudanar shekaru uku da suka gabata.

An shafe tsawon shekaru biyu ana kokarin rubuta sabon kundin tsarin mulkin wanda ya haifar da baraka tsakanin sauran Jam’iyyun siyasa da Jam’iyyar Ennahda ta ‘Yan uwa musulmi da ke shugabanci a kasar.

Ana ganin sabon kundin tsarin Mulkin tamkar cin gajiyar juyin juya hali ne da mutanen Tunisia suka gudanar a watan Janairun 2011 inda suka kawar da gwamnatin Zine El Abidine da ya kwashe shekaru da dama yana shugabanci.

A kasar Tunisia ne aka fara zanga-zangar kin jinin gwamnatocin kasashen Larabawa, amma har yanzu a kasashen Libya da Masar hankuli bai kwanta ba bayan kawar da Ghaddafi da Mubarak.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.