Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mutanen Zimbabwe sun yi tozali da Mugabe

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya fito a bainar Jama’a a birnin Harare a karon farko wanda ake rade radin yana fama da matsananciyar rashin lafiya. Amma Mugabe wanda ke shirin cika shekaru 90 a duniya a ‘yan kwanaki masu zuwa, ya fito a yau Litinin domin zaman makokin kanwarsa da ta rasu.

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe.
Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe. REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Wannan dai ya zo ne a daidai lokacin da al’umma a ciki da wajen kasar ke ci gaba da yada jita-jitar cewa shugaban na fama da matsananciyar rashin lafiyar da ta sa sam ba zai iya fitowa domin tafiyar da ayyukan shugabancin kasar ba. Wasu ma cewa suke yi ya mutu.

Ko a farkon wannan shekara dai rahotanni sun ce shugaban, ya share tsawon makwanni biyu a kasar Singapore a wani abu da ake kallo a matsayin ganawa da likitocinsa.

Mugabe mai shekaru 89 na haihuwa, tun lokacin da Zimbabwe ta samu ‘yancin kai a 1980 daga Turawan Ingila ya ke shugabancin kasar.

Sakamakon yadda jaridu da kuma sauran jama’a suka soma bayyana shakku dangane da lafiyar shugaban, Mai magana da yawun Robert Mugabe George Charamba, ya ce ai ba wani bakon abu ba ne idan har shugaban kasa ya share tsawon kwanaki ba tare ya fito a bainar jama’a ba, domin kuwa a kowane wata na Janairu shugaban na zuwa hutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.