Isa ga babban shafi
Zimbabwe

An rantsar da Mugabe wa’adi na 7 a Zimbabwe

Robert Mugabe ya karbi rantsuwar aiki a matsayin shugaban kasar Zimbabwe wa’adi na bakwai bayan nasarar da ya yi a zaben shugabancin kasar na ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata.

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe,
Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, REUTERS/Philimon Bulawayo (
Talla

A yau Alhamis ne aka rantsar da shugaba Mugabe, amma babban mai adawa da shi Morgan Tsvangirai ya tsaya kan bakarsa na lalle an yi magudi a zaben da ya dawo da Mugabe saman madafan iko tare da kauracewa gangamin bukin rantsar da shugaban.

An samu tsaikun bukin rantsar da Mugabe saboda karar da Tsvangirai ya shigar domin kalubalantar sakamakon zaben a kotun kundin tsarin mulki.

Amma a ranar Juma’a ne Tsvangirai ya janye karar yana mai zargin ba za’a ya adalci ba.

Tuni dai kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da galabar da Mugabe ya samu a zaben na watan yuli, lamarin da ya sa Kakakin jami’iyar ZANU PF mai mulki Rugare Gumbo ya ce a yau suna a cikin farin ciki saboda ana rantsar da shugaban da jama’ar kasar suka zaba.

Rugare ya ce galabar da Mugabe ya samu, wata babbar nasara ce a kan ‘yan mulkin mallaka, yana mai cewa ai wannan nasara ba wai ta takaita ne kawai a cikin kasar Zimbabwe ba, amma har zuwa sauran kasashen Afrika da kuma masu fatar samar da adalci a duk inda suke a duniya.

Mugabe ya lashe zaben Zimbabwe ne da rinjayen kuri’u kashi 61 fiye da abokin hamayyar shi Morgan Tsvangirai.

An haifi Robert Gabriel Mugabe ne a ranar 21 ga watan Farbrairun shekarar 1924.

Mugabe kuma yana daya daga cikin yan kungiyar kwato ‘yancin kan Zimbabwe, kuma Mugabe ya sami nasarar zama Firaministan kasar a shekarar 1980, kafin zama shugaba mai cikakken iko na farko a kasar a shekarar 1987.

A cikin shekarun 1960 mugabe ya yi suna a kasar, lokacin da ya ke rike da mukamin Sakatare Janar na jama’iyyar shi ta ZANU-PF, lokacin da take dauki ba dadi da gwamnatin tsiraru fararen fata ta Ian Smith.

Mugabe ya yi a zama fursunan siyasa tsakanin shekarun 1964 zuwa 1974. Kafin daga bisani ya bar kasar, inda ya ci gaba da adawa da Gwamatin daga kasar Mozambique.

A shekarar 1980 ne Mugabe ya tsaya takara, ya kuma zama Friminista kasar a zaben kasar na biyu, da bakaken fata masu rinjaye suka kada kuri’a, kuma a ranar uku ga watan Agustan wannan shekarar ya lashe zaben shugabancin kasar karo na Bakwai a jere.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.