Kotun kolin Zimbabwe ta amince da sakamakon zaben kasar
Kotun Kolin kasar Zimbabwe, ta amince da cewar, shugaba Robert Mugabe ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a karshen watan da ya gabata.
Wallafawa ranar:
Mai shari’a Godfrey Chidyausiku, ya bayyana cewar an gudanar da zaben ne ba tare da wani magudi ba, hukuncin da yanzu ya bada damar rantsar da shugaban a wa’adi na bakwai.
A karshen makon day a gabata kungiyar kasashen kudancin Afrika ta SADC ta amince da sakamakon zaben kasar, inda ta nada Mugabe a matsayin mataimakin shugabar kungiyar.
Jam’iyar adawa ta MDC na ikrarin zaben na tattare da magudi da dama inda ta janye wata kara da ta shigar a gaban kotu tana mai ikrarin cewa ba za a musu adalci ba.
A wannan makon ne ake sa ran za a rantsar da shugaba Mugabe, dan shekaru 89 a wa’adi na bakwai inda zai sake kwashe shekaru biyar yana mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu