Isa ga babban shafi
Najeriya

Jonathan yana da ‘Yancin tsayawa takarar zabe a 2015-Maku

Ministan yada labaran Najeriya Labaran Maku wanda ke zantawa da manema labarai a game da cika shekaru 100 da hadewar yankunan Arewaci da kudanci a matsayin Najeriya, yace a karkashin dokokin Najeriya ba inda aka haramtawa shugaban kasa Goodluck Jonathan damar sake tsayawa takara a zaben 2015.

Ministan yada labaran Najeriya Labaran Maku
Ministan yada labaran Najeriya Labaran Maku sahararepoters
Talla

Mista Maku yace yayata batun haramcin tsayawa takara ga Jonathan, ba abinda zai haifar face fitina a tsakanin al’ummar Najeriya.

A cewar Maku, babu wani shugaba da aka taba yi a Najeriya da ya yi ayyukan ci gaba fiye da Jonathan, yana mai jaddada cewa ya zama dole Jonathan ya nemi wa’adi na biyu saboda ayyukansa na alheri ga ‘Yan Najeriya.

Har yanzu dai Shugaba Goodluck Jonathan wanda ya fito daga yankin Niger Delta be fito fili ya ayyana kudirinsa ba na neman wa’adin shugabanci na biyu duk da kalubalen siyasa da shugaban ke fuskanta daga Jam’iyyasa ta PDP bayan wasu gwamnoni da ‘Yan Majalisu sun fice jam’iyyar.

Akwai dai dimbin matsaloli da suka dabaibaiye Najeriya musamman matsalar tsaro da cin hanci da rashawa amma a cewar Labaran Maku, gwamnatin Goodluck Jonathan ta samar da ci gaba fiye da gwamnatocin da suka gabata tun zamanin mulkin Gowon, yana mai danganta yadda gwamnatin ta tunkari matsalar tsaro da tattalin arziki.

00:42

Labaran Maku

A kwanakin baya a garin Kaduna, a lokacin da ya ke jawabi a wani taro, Labaran Maku, ya yi kira ga Mutanen Arewa su yi watsi da siyasar kabilanci su dawo su goya wa Jonathan baya a zaben 2015.

A hirarsa da Rediyo Faransa yace be ga laifin da Jonathan ya yi ba da za’a haramta masa neman shugabanci wa’adi na biyu.

“Wace doka ce ta hana shugaban kasa ya tsaya zabe” inji Labaran Maku.

Shugaba Jonathan dai yana fuskantar kalubale musamman daga mutanen yankin arewaci saboda yadda ya yi watsi da wata yarjejeniyar karba-karbar shugabanci tsakanin yankin kudanci da arewaci ta jam’iyyarsa ta PDP.

Maku yace babu mutumin arewa da za’a zaba kuma ya ki amincewa ya yi mulki wa’adi na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.