Isa ga babban shafi
Algeria

Shugaba Bouteflika zai yi takarar shugabancin kasar Aljeriya

A kasar Aljeria, Jama’iyya mai mulki ta FLN, ta bayyana shugaban kasar maici, Abdulaziz Boutaflika a matsayin dan takarar ta, a zaben shugaban kasa da za a yi a shekara mai zuwa ta 2014. Jama’iyyar ta National Liberation Front ko FLN, ta bayyana shugaba Boutaflika a matsayin dan takarar ta, duk da rade radin da ake yi na rashin lafiyar shugaban, mai shekaru 76 a duniya.Lamarin rashin lafiyar shugaban ya fito fili ne a farkon wannan shekarar. Lokacin da ya shafe watanni 2 a wani asibitin kasar Faransa, sakamakon ciwon bugun zuciya, da ya yi fama da shi.Shekaru 14 Abdoulaziz boutaflika ya shafe a kan karagar mulkin kasar Aljeria, kuma ya shafe fiye da shekara guda bai yi jawabi ga ‘yan kasar ba, sakamakon jinyar da yake yi, inda wasu ke rade radin, baya iya magana.Juyin juya halin kasshe larabawa, da ya yi sanadiyyar kifar da gwamnatocin kashen na larabawa da dama, ya samo asali ne daga kasar ta Aljeria, sai dai har yanzu kasar bata gargiza da wadancan tashe tashen hankulan ba. 

Shugaban kasar Aljeriaya, Abdelaziz Bouteflika
Shugaban kasar Aljeriaya, Abdelaziz Bouteflika REUTERS/Louafi Larbi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.